Zargin Madigo: Gaskiya Tayi Halinta – An Gano Bayanan Sirri A Wayar Amal

0 291

ADVERTISEMENT

Bayan duk kace nace daya auku akan rigimar hadiza gabon da amina amal kan wani hoton rubutu (screenshot) da amal ta daura a shafinta, akan tana zargin wata da madigo. Kuma akasan hoton tace wata ta nemeta da aikata madigo. (Amma kuma bata bayyana sunan mutumin ba).

Screenshot da Amina Amal ta daura a shafinta wanda shine musabbabin hada wannan fada
Rubutun da Amina Amal tayi, da ke tabbatar da wanda yayi wannan rubutun ‘yar madigo .kuma hadiza gabon ce tayi.

Anan fa mutane ke zargin, tunda hadiza gabon tai wa amal dukan tsiya batare da amal ta bayyana sunan kowa ba, to akwai lauje cikin nadi. Wasu kuma cewa suke, to meyasa ta tsargu ?

Wasu sun gaskata maganar amina amal, wasu kuma na ganin laifin hadiza gabon kan dukan da tayi mata.

Ana cikin wannan hargitsin ne, A ranar 11 ga watan afrilun 2019, fittacciyar jaruma hadiza gabon ta wallafa videon duka hirarsu da sukayi da ita da Amina amal tun daga 04- ga watan october, 2017. kusan shekaru biyu kenan.

Bayan na karanta wannan hirar tasu gaba daya, Anan na fahimci cewa, Ita Amal dince ta fara nuna tana mutukar son gabon, kamar yadda videon ya nuna. kuma wannan screenshot (wato hoton rubutun da ta wallafa a shafinta, wadda shine mussabbabin hada wannan husumar, gutsuroshi tayi a wata hirar da sukayi da hadiza gabon tun shekarar bara (Wato 2 ga watan march shekarar 2018).

Hasalima, a videon da hadiza gabon ta wallafa a shafinta, zaku ga ita gabon din na watsi da amal, idan ta tura mata sako ba kasafai take mayar mata da amsa ba.

ADVERTISEMENT

Sannan vedion ya nuna su ba kawaye bane don hirar tasu bata yi kama da na kawaye ba….. gaisawa kawai sukeyi, nan ma, kuma ita amal din ta fi yawaita turowa gabon sakuna

Ha ilau, videon hirar tasu yayi nuni da yadda ita amal din ta damu gabon ta bata lokaci su gana don ta fada mata wata muhimmamiyar magana!(wannan dai duk cikin videon hirar tasu ya wakana amma mutane da dama na ikrarin cewa lallai gabon ta goge wasu wurare)

Duk cikin wannan chakwakiyar da ya wakana a dan kwanakin nan, gaba dayansu nada laifi, ita amal bai kamata ta yanko hira daga cikin hirar su da sukayi ba, hakan yasa aka canza ma’anar kalmomi. wannan dalilin yasa gabon tsarguwa don tasan hirar da sukayi ta yanko ta daura.

Inda Hadiza Gabon tayi kuskure shine, dukan amal da suka taru sukayi, koma me amal tayi mata, ba kazafi ba, imma abin da ya fi haka ne, bai kamata ki dau doka a hannunki ku kama yarinya ke da kawayenki kuyi mata duka ba har ma ku daura shi a social media kowa ya gani ba..

Duk kawar da ta baki wannan gurguwar shawawar wallahi ta cuce ki….da kinbi ta yadda ya kamata ba ku ci zarafin ta ba! .

Sai bango ya tsage har kadangaru ke samun wurin shiga. Da tun farko da kika ga ta fara miki kalaman banza wato ta fara wuce gona da iri, Sai kiyi blocking dinta kawai, da bata samun fuskan ci gaba da yi miki magana ba.

Ga shi ta miki sharri, ta kuma ta bata miki suna, kuma kin kwan a ciki. Har lawyoyi 15 sun tsaya mata kan cin zarafin da kuka yi mata.

Ga screenshot din hirar ta su kasance da har tasa gabon fadar wannnan kalmomin, don ta fadeshi ne ba da wata manufa ba.

ADVERTISEMENT

Leave A Reply

Your email address will not be published.