Rikici ya barke tsakanin matan Kannywood biyu akan soyayyar wani katon Arne Senata Dino Melaye

0 147

ADVERTISEMENT

  • Rikici ya barke tsakanin Fati Muhammed da Teema Makamashi akan soyayyar Sanata Dino Melaye
  • An dai ga Teema Makamashi tana habaici a shafinta na Instagram inda
  • Duka ‘yan matan sun yiwa Sanatan waka da fasta ta siyasa sun kai masa, inda ya dauki hoto da kowaccen su

Wani rikici da ya barke tsakanin matan Kannywood guda biyu Teema Makamashi da Fati Mohammed, inda suke rikici akan Sanatan jihar Kogi ta Yamma Sanata Dino Melaye.

Kalli cikakken videon fadan nasu anan👇👇 don ku fi ganewa

Rikicin ya samo asali ne lokacin da Teema Makamashi take gargadin Fati Mohammed akan kwaikwayenta da tayi wurin yiwa Sanatan waka.

Ga abinda Teema Makamashi kuma ta rubuta a shafinta na Instagram:

ADVERTISEMENT

“Keda samun soyayyarsa sai dai ki gani daga nesa”

Tauraruwar Teema Makamashi wacce ita ce ta fara yiwa Sanata Dino Melaye waka, tayi wannan habaicin ne ga Fati Mohammed wacce ta kwafeta.

Teema tayi rubutun ne a shafinta na Instagram inda ta cigaba da cewa, “Ga wani sabon salon shima idan zaki yi, banda waka, tunda kome nayi sai kinyi, kina tare da bakar wahala indai ni zaki dinga kwaikwaya.”

Tauraruwar ta saka hoton fastar siyasa da tayi wa Sanatan a shafinta na Instagram a lokacin da tayi wadancan habaicin.

An ga Fati Mohammed ta yiwa Sanata Dino Melaye waka da kumaa fasta ta siyasa.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KaSCR0Vwn9HHJI2DSszGak

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/idongari_tv

Twitter: https://twitter.com/idon_garitv

Instagram: https://instagram.com/idongari_tv

Youtube: https://www.youtube.com/idongaritv

Source : https://legit.ng

ADVERTISEMENT

Leave A Reply

Your email address will not be published.