Ni Sa’ar Uwarka Ce – Hadiza Gabon ta mayar da martani ga wani da yace mata ta tsufa

0 79

ADVERTISEMENT

Mun sami labarin yadda fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Hadiza Gabon ta dinga sirfawa wani mutumi zagi saboda ya kira ta da tsohuwa

Mutane da yawa sun goyi bayan abinda jarumar tayi, inda wasu kuma suke ganin abinda tayi din bai dace ba.

Danna nan πŸ‘‡ don Kallon video ko cigaba da karatu

ADVERTISEMENT

A Kwanan nan ne dai fitacciyar jarumar fina-finan Hausan nan Hadiza Gabon ta dora wani sabon hotonta akan shafinta na sada zumunta na Istagram, domin masoyanta da abokan arziki su kalla.

Bayan wannan hoton da tasaka jama’a da dama daga cikin masoyanta sun yaba da kyawun da ta yi, wasu ko sukar shigar da tayi sukayi inda sukace ya kamata ta rufe jikinta idan zata dau hoto ta daura duniya ta gani….

Kwatsam sai aka jiyo wani daga cikin masu bin shafin nata mai suna musa abdulhadi muhammed yayi rubutu a kasan hoton nata da ta daura inda yace a turance : “You looked so beautiful but you are old” ma’ana “Kinyi kyau sai dai fa amma kin tsufa.”


Hakanne ya tunzura fitacciyar jarumar ta maida masa martani a turance kamar haka: “I am your mother’s mate!” ma’ana “Ni sa’ar uwarka ce!”


Sai dai kuma bayan jarumar ta mayarwa da mutumin martanin, wasu daga cikin masoyanta sun dan yi korafi akan furucin nata, inda suke ganin abinda ta fada din bai kamata ba. Yayin da wasu kuma suke ganin abinda ta yi din yayi daidai.

Dama sarakan magana sunce idan kasan abin da zaka fada to baka san amsar da za’a mayar maka ba.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KaSCR0Vwn9HHJI2DSszGak

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/idongari_tv

Twitter: https://twitter.com/idon_garitv

Instagram: https://instagram.com/idongari_tv

Youtube: https://www.youtube.com/idongaritv

ADVERTISEMENT

Leave A Reply

Your email address will not be published.