Mahaifin Kwankwaso ya yi biyayya ga umarnin Ganduje Inda ya janye biyyayarsa ga sarkin Kano Sanusi II.

0 48

ADVERTISEMENT

Musa Kwankwaso, hakimin karamar hukumar Madobi kuma mahaifi ga tsohon gwamnan jihar Kano, engineer Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, ya janye biyayyar sa ga sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

A kwanalin bayan nan ne gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya rattaba hannu a kan dokar masarauta da majalisar dokokin jihar tayi wa garambawul.

Daga cikin gyaran da aka yiwa dokar akwai bukatar kara kirkirar sabbin masarautu hudu da sarakuna masu daraja daya da ta sarkin Kano.

Sabbin masarautun da dokar ta amince da kirkirar su akwai, Bichi, Gaya, Karaye da Rano.

A ranar Asabar ne gwamna Ganduje ya rantsar da sabbin sarakunan masarautun tare da basu sandar iko, sannan ya umarci duukan masu rike da sarautar gargajiya da malaman addini da suyi mubaya’a ga sabbin sarakunan yankin da suka tsinci kan su.

Sabbin sarakunar kano

Sabanin wasu masu rike da sarauta da suka yi murabus ko kin yin biyayya ga sabbin sarakunan, Musa Kwankwaso ya jagoranci kafatanin masu rike da sarauta dake karkashin sa wajen kai ziyarar yin muba’a da biyayya ga sabon sarkin Karaye, Ibrahim Abubakar II, da masarautar karamar hukumar Madobi ta koma karkashin ikon sa.

ADVERTISEMENT

Wannan ziyara ta Musa Kwankwaso ta nuna cewar ya yi biyayya ga umarnin Ganduje, ya janye biyayyar sa daga tsohuwar masarautar Kano.

Ku biyo mu a Facebook: facebook.com/idongaritv

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>>

https://chat.whatsapp.com/KaSCR0Vwn9HHJI2DSszGaI

Youtube.com/idongaritv

Instagram.com/idongari_tv

Twitter.com/idongari_tv

ADVERTISEMENT

Leave A Reply

Your email address will not be published.