Mace Musulma ‘yar Arewa Tana Nemawa ‘yan Madigo Da Luwadi ‘yanci

0 171

ADVERTISEMENT

INNALILLAHI WA INNAA ILAIHI RAJI’UUN

lokaci yayi da zan jagoranci neman bayar da ‘yanci a duk kasashen duniya ga ‘yan Luwadi, da ‘yan Madigo inji Amina j mohammed.

Duniya Tazo Karshe, Labari mafi muni da Tayar Da Hankali Daga Gurin ‘yar uwarmu Musulma Mataimakiyar sakataren majalisar dinkin duniya Hajiya Amina j Muhammad inda tace
lokaci yayi da zata jagoranci neman bayar da ‘yanci a duk kasashen duniya ga ‘yan Luwadi, da ‘yan Madigo.


Amina j muhammad dince ta daura hoto da tutan ‘yan lesbian kana ta rubuta sanarwar a shafinta na Twitter tana mai cewa lokaci yayi da zata jagoranci neman bayar da ‘yanci a duk kasashen duniya ga ‘yan Luwadi, da ‘yan Madigo, da masu zina da dabbobi da sauransu, wadanda a kungiyance ake kiransu da “Lesbian, Gay, Transgender, Bisexual and Queer” (LGTBQ).

Kalli Video Anan πŸ‘‡πŸ‘‡Tace “Let’s #Standup4HumanRights to #LeaveNoOneBehind & ensure a life of dignity for all. #Pride
#AcceptanceMatters

ADVERTISEMENT


Kamar yadda kuka yi tsammani, wannan sanarwa nata ya sha suka sosai daga wurin musulmai har ma da wasu wadanda ba musulman ba. Ga kadan daga cikin comment masu daukar hankali da aka martani dashi a kasar wannan sanarwa nata.


Ga ra’ayin wani mai pagin hausa loaded
Yace ” Muna raye a duniya wannan abin zai faru? innalilLahi wa innaa ilaiHi raji’uun!, Malamai aiki ya sameku, dole ku tashi ku fara wa’azi da khudubah akan abinda wannan matar tayi alwashin aiwatarwa a duniya, duk wani Malami ko shugaba mai fada aji da yayi shiru akan wannan mummunan kuduri wallahi yaci amanar al’ummah kuma yaci amanar Musulunci.


Amina munyi hannun riga dake, wallahi babu mu babu ke har abada matukar baki janye wannan mummunan kuduri ba, domin kin taro fada da Allah (SWT) Muna dauke da sako zuwa gareta, duk wanda yake da kusanci da ita muna neman alfarma ya isar mata da sakon da zamu wallafa

Yaa Allah mun kawo karansu gareKa, Ka isar mana tsakaninmu da su!

Engr yasir yusuf arafat yace : “ko a mulkin jonathan nigerian taki yarda ta baiwa ‘yan madigo ‘yanci …amma sai gashi musilma ‘yar uwarmu kuma ‘yar arewa tayi haka…gaskia kin bamu kunya…iliminki ya kaiki ga halaka.

Wani Sufiyanu yace ” mace kuma yar arewa ta ke goyon bayan yan madigo bayan alqur’ani ya hana gaskia kin bami kunya.

Menene Ra’ayinku Game da Wannan kudirin da hajiya Amina ke son aiwatarwa a nigeria??????

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KaSCR0Vwn9HHJI2DSszGak

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/idongari_tv

Twitter: https://twitter.com/idon_garitv

Instagram: https://instagram.com/idongari_tv

Youtube: https://www.youtube.com/idongaritv

ADVERTISEMENT

Leave A Reply

Your email address will not be published.