Iyaye! Ko kunsan Akasarin Kananan Yara ‘Yan Uwansu Na jini Ne Ke Soma Lalata Dasu?

0 75

ADVERTISEMENT

Binciken masana

Ummancy Umar
Tonga Abdul

Al’amarin yanada bada tsoro, akwai takaici a cikinsa. Cin amana shi ne abunda wannan binciken ya gano dangane da yadda ‘yan uwa na jini ne suka fi yawaita bata yara mata da aka aminta dasu aka saki jiki da su.

Daga watan Janairun data gabata zuwa wannan Janairu sabuwar shekara ta 2019, dani da matata munyi aikin baiwa samari da ‘yan mata wanda yawansu a cikin littafin mu na adana irin wannan sunayen suka kai dubu goma sha biyar da dari uku da goma sha daya. (15,311).

A cikin wannan jimmilar dubu takwas da hamsin mata ne. Dubu biyar da dari bakwai ‘yan mata ne wadanda basu haura shekaru 25 ba. A cikinsu dubu hudu da dari biyu da hamsin sun taba zina. Kana dubu uku da dari shida ‘yan uwansu na jini ne suka soma yin zina dasu. Wannan yasa muka yanke shawarar fitowa da wannan binciken namu domin kowa ya gani musamman iyaye, domin nazari da kuma daukan mataki na kiyaye afkuwar ire iren wannan lamarin.

Babu shakka addini da al’ada sun baiwa ‘yan uwa damar kusantar ‘yan uwansu koda kuwa mata da maza ne. Da wannan ne shima Shedan yayi alkawarin sai yayi amfani da wannan damar domin ganin ya cusa son zuciya a tsakanin muharramai domin cutar dasu.
Akasarin wadannan ‘yan matan basu wuce shekaru 10, zuwa 13 a lokacin da aka musu wannan aika aikan ba. ” bana mantawa ni dai kanin mahaifiyata ne ya soma lalata dani, tun ban yi wayo ba yake haba-haba dani har lokacin da na soma wayo. Kamar yadda kika ganni inada girman jiki domin wasu idan na fadamusu shekaruna basa yarda saboda yanayin jikina. Nayi saurin fito da nonuwa tun kamin na soma al’ada.

“Akwai wata rana ne da shi kawuna ya zo gidanmu a lokacin kuwa babu kowa a gidan sai ni kadai. Kuma daman can ya sha yi mini wasannin banza yana taba mini nonuwa tun ma bam kai haka ba. A wannan ranan ne dai ya samu yayi zina dani. A gaskiya ba wai ya tilastani bane, domin tunda na soma wayo na gane yana sha’awata duk da nasan kanin mahaifiyata ne, yakan mini wasannin da ni kaina inaso idan muka faki idanuwan mutane. Kuma daga wannan ranar na soma sanin namiji da dadinĺsa”. Wannan wata ce daga cikin wadanda muka baiwa shawara.

Binciken namu ya nuna cewa cikin wadannan ‘yan matan da ‘yan uwansu na jini suka soma lalata dasu, kannen iyayensu mata sunfi yawa. Domin kashi 70 cikinsu kawunansu ne suka soma farwa budurcinsu. Wanda masu karatu zasu fi tunanin ‘yan uwansu na ‘yan wa da Dan kani ne zasu fi aikata hakan, amma ina, wannan sune ma suka zo ana uku baya ga mazan iyayensu mata.

Sai ‘ya’yan yayyu ko kanne a na uku da kannen mahaifa sai kadan daga wadanda iyayensu da suka haifesu ne suka soma yin zina dasu.

Wannan yasa muka sake dubawa do mu ga ko mai yasa su kannen iyaye mata suka fi yawa cikin mutane masu lalata da jininsu. Sai muka fahimci cewa irin yarda da amana da uwa take yiwa Dan uwanta yasa maza masu wannan halin suke cin wannan amanar.

A duk lokacin da aka ce ga ‘yarku ta fita da Dan kanin mijinki ko Dan ‘yarsa ko kanwarsa, ana kaiwa wani lokaci hankalin iyayen bazai samu natsuwa, cikin abunda zai shigo ransu kuwa harda tunanin zina a tsakaninsu. Haka nan, da za ace kun fita kun barsu a gida su biyu nan ma babu kwanciyar hankali kuna tunanin komai na iya faruwa.

Amma idan da kanin matarka kane ko kanin ka babu wani abunda zai zo maka na tunanin wani al’amari irin wannan ko da kuwa dukkaninsu kusan shekarunsu guda ne sabanin Dan wanka ko kaninka ko na dan wan matarka. To fa anan gizo ke sakar.

Da wannan aminta ne da kuma haramcin dake tsakaninsu yasa ake kauda kai.

“Ni kanin mama na har ciki yayi mini. Domin tun ina karama yake dorani akan cinyansa har na soma girma sai ya rika goga mini azzakarinsa a gabana kuma ya tsoratani kada na fadawa kowa.

ADVERTISEMENT

Yana matukar nuna mini kauna, kuma iyayena sunyi matukar yarda da shi. Shike kaini makaranta shike daukoni.

Da zani ummura da aikin Hajji dashi aka hadamu. A lokacin da na nace inason zuwa Dubai naga garin, saboda yadda dashi aka hadamu aka bamu kudin hotel na kwanaki 10 kowa da dakinsa amma a daki guda muke kwana.

” Kuma bazaka taba ganin wasu alamun cewa akwai wata alaka ko soyayya a tsakaninmu ba.

Domin ana ganin shine mutumin da nake shakka da tsoro. iyayena kuma basusan shine mutumin daya lalatani ba. Ya zama bana iya barci idan ba a jikinsa ba, gaskiya abunda yasa ma nazo wajenki Aunty Ummancy, inaso ne ki bani shawarar yadda zan daina sonshi. ina son yin aure tunda nasan bazan aureshi ba”. Inji wata da muk sakaye sunanta.

Masu auren maza sunada yara mata suma suna cikin wannan masifar, domin binciken ya tabbatar da cewa mazajen wasu matan sun taimaka matuka wajen lalata musu yara duk kuwa da haramcin auratayya dake tsakaninsu.

“Ina da shekaru 10 a duniya mahaifiyata ta aure mijinta bayan mahaifina ya rasu. Tun bamu shekara a gidansa ba ya soma nuna alamun yana son yin zina dani. Da yake shi ba wani mai tsauri bane, yana da son mutane kuma yana daukata tamkar ‘yar cikinsa duk da yanada wasu yara matan amma basu kaini shekaru ba.

Yana daukanmu yaje ya mana sayayya amma nawa daban yake mini. Tun ban fahimceshi ba har dai na soma fahimtarsa.
Akwai wata rana da mahaifiyata ta fita unguwa nayi wanka ina shafa mai kawai sai naji ana wasa da nonuwana, kamin dai nace wani abu aikin gama ya gama, kuma daga wannan ranar lokaci zuwa lokaci muna yi, sai dai da kansa yace mu daina. kuma gaskiya ya daina amma ni kuma na saba, inada samari da nake samunsu idan ina sha’awa, sai dai kamar yadda na fadamiki yanzu na samu wanda zan aura shine na miki bayanin matsalar da yanzu ake ciki”. Wannan ma mijin mamanta ne ya soma lalata da ita.

Hirarrakin suna da yawa, Sai dai abin bukata shine iyaye su fahimci irin hadarin da suke ciki, domin sanya idanuwa a inda y kamata su saka idanuwan. Sai kuma, irin wasu da yayunsu ciki daya ne suka soma lalata dasu. su kuma yaya za ayi? Da akwai ‘yan mata uku cikin wadanda muka baiwa shawara. biyu cikinsu ubansu da suka haifesu su suka lalatasu, guda kuwa wanta ne uwa daya uba daya.

Bayaga mata, cikin maza suma mun samu wadanda kannen iyayensu ne suka soma koya musu zina, wasu kuwa ‘yan uwan iyayensu ne suke yi luwadi dasu.

Manufar fito da wannan binciken cikin harkar mu na bada shawara shine dai, al’umma su fahimci babu abunda zuciya bazai iya aikatawa ba idan aka baiwa shedan damar yin hakan. Yanada da kyau iyaye suyi iya abunda zasu iya yi domin sauke hakkin dake kansu na baiwa ‘ya’yansu da yaran dake karkashin su kulawarsu.

Kada iyaye su dauka wane bazai iya yin haka ba, haka kuma kada iyaye suyiwa na kusa dasu mummunar zato ko fahimta, illa dai wannan binciken yana son ya ankarar da iyaye ne don su fahimci watakila yanzu haka akwai abubuwa marasa kyau dake gudana a cikin gidajensu, ko dai basu maida hankali wajen ganowa ba, ko kuma an tsorata wadannan yaran da ake cutarwa na kada suyi magana.

Allah Ya shirya, Ya kuma tsaremu da iyalanmu Ya bamu ikon sauke nauyin tarbiyan dake kanmu Ya kuma sa mufi karfin sha’awan mu.

════════════════════

Islamic medical center
・ Sirrin・ℳaιιakar・ℳiji �
WhatsApp GroupÇhart
📳 +2347066620951

ADVERTISEMENT

Leave A Reply

Your email address will not be published.