Idan Namiji Na Cina Sai Na Tuna Hadiza Gabon kafin in kawo Cewar Amina Amal

0 582

ADVERTISEMENT


Rigima ya barke tsakanin jaruman kannywood biyu, jaruma Hadiza Gabon da kuma jaruma Amina Amal kan zargin madigo da amina amal kewa hadiza gabon inda har tayi ikrarin cewa hadiza gabon ta nemeta.

Abinda Ke Ciki

  • Jaruma Amina Amal tayi barazanar tona asirin wata ‘yar madigo da ba’asan ko wacece ba a shafin ta na sada zumunta.
  • Hadiza Gabon ta yiwa amina amal dukan tsiya kan cewa tayi mata kazafi da aikata madigo.
  • Reshe ya juye da mujiya bisa dukan da hadiza gabon tayi wa amal inda wasu da dama ke cewa “Tabarmar Kunya Dama Da Hauka Ake Nadeta.”

Asalin Abinda Ya Faru A Tsakaninsu Tun Daga Farko

A ranar talata 9 ga watan aprilun 2019, wani sabon faifen video ya bayyana a shafukan sada zumunta inda jaruma hadiza gabon take dukan jaruma Amina Amal akan cewa ta ce mata ‘yar madigo. Sai dai ita amina amal tayi ikrarin cewa ba da ita take ba don bata ambaci sunan kowa a rubutun da tayi ba.

A cikin bidiyon, an nuna jaruma hadiza gabon na shararawa amal mari kuma an rika jin muryar hadiza Gabon tana cewa a bari ta yiwa Amal dukan tsiya saboda wai tayi mata sharri yayin da ita kuma Amal tayi zugum zaune a kan gado tana shan duka.

Amal din ta rika fada wa Gabon cewa ta yafe mata domin kuskure ne kuma sharrin kwaya ne inda hasali ma ta ce ita ba ta san lokacin da ta aika wannan sakon ba.

Ga videon a kasa,

Saurari Videon Cikakken Abinda Ya Faru (idan baka so ci gaba da karatunka)

Yadda Rigimar Ta Fara

Bayan Amina Amal tayi posting wani hotonta daya bayyana tsiraicinta. Dayawa daga jaruman kannywood sun yi mata fada da nasiha. Wasu kuma zaginta sukayi. Ciki har da jaruma Aisha Aliyu Tsamiya, Hadiza Gabon da dai sauransu inda Gabon tace “you are verry stupid wallahil azim kuma wannan abinda kike yi bazai sa ki yi suna ba.”

Duk da wannan fada, zagi da nasiha da akayi mata. Amina Amal ba ta goge wannan hoton ba. sai ma wani irinshi ta sake daurawa.

Bayan wasu ‘yan awanni sai ta daura screen shot din wani rubutun da aka mata,² wanda ba’a san wacece tayi mata shi ba, don ta goge sunan marubuciyar, inda aka ce ” insha Allah zan dawo, ina sonki a kusa dani, u will be fine insha Allah. Zan kaiki wani wuri ki huta na kwanaki.”

Sai kuma ita amina amal ta mayar da martani ga wadda ta turo mata rubutun inda akasan wannan screenshot din da tasa a pejinta tace “gwamma ni, ba cin mata nake yi ba sai dai ace ina dressing mara kyau ko kuma ace ni karuwa ce. Duk wanda yace ni karuwa ce baida hujja sai dai yace daga dressing dina. Inna sake posting abu a pejina kika zageni to wallahi sai na fadawa duniya cewa kema ‘yar iska ce.”

Ta kara da cewa ” Har yanzu ina ganinki da mutunci amma idan baki rike girmanki ba, nima bazan girmamaki ba. Kawai kiyi abinda yake gabanki . Har iyau ina da message din da kika min kuma kika ce kar in fada wa kowa saboda kina nunawa duniya ke mutuniyar kirki ce a zahiri. Kada ki sake zagina inba haka ba zaki sha mamaki.”

ADVERTISEMENT

Bayan Amal tayi wannan rubutun a kasa hoton, nan kan mutane ya daure, suka fara tunanin da wa amal take yi kuma?

Sai can bayan kwana biyu, wannan videon dukan da hadiza gabon tayi wa amal ya fito social media. Kancewa amal tayi mata kazafin aikata madigo. Amal ta musa zancen da cewa ai ita ba ta ambaci sunan kowa ba. Daga baya dai wasu sunce, tursasa amina amal akayi har ta ba da hakuri.

Wannan video da ya bayyana, ya jawo cece kuce sosai a shafukan sada zumunta inda wasu suka gaskata maganar Amal da cewa, rubutun da tayi akwai kamshin gaskiya a cikinta, saboda ba ta ambaci sunan kowa ba, amma kuma meyasa ita hadiza gabon ta tsargu bayan ba ita kadai ba ce jarumar da ta zagi amina amal bayan ta wallafa hoton tsiraicin nata. Awai jarumai dayawa da suka zagi wannan shiga nata kamar Aisha Tsamiya da sauransu, Su mesa basu tsargu ba sai ita.

A cikin faifen videon da ya bayyana a social media akwai wani furuci da hadiza gabon tayi inda take cewa Amina “Ranar da kizo gidana Amina! ce min kikayi idan kina kwanciya da namiji sai kin tunani kafin ki kawo.”! Toh fa! Anan ne wasu ke ganin cewa me hadin ita amal da gabon har take zuwa gidanta.

Daga jarumai, har ‘yan kallo kowa na ganin laifin hadiza gabon inda da dama ke fadin cewa abinda tayi bashi da maraba da borin kunya. Don in tana da gaskiya mai zai sa ta tubure tai ta dukan ‘yar mutane haka, kamata yayi tayi watsi da batun tunda bata kama sunanta ba. inda Wasu kalilan daga masoyan ta kuma na ganin cewa abinda tayi yayi dai dai kuma hakan kadai ne sai sa ta wanke kanta daga zargi.

Wannan daukar doka a hannu da gabon tayi ya jawo maganganu sosai daga wajen jama’a inda wasu ke kokarin janyo hankalin lauyoyin hukumar kare hakkin dan adam akan da su dauki mataki akan wannan abin da ya faru.


Wasu kuma na ganin ta ci zalin Amal ne kawai don ta fita kudi, ta fita daukaka, kuma ta fita sanin manya, shiyasa take so tayi amfani da wannan daman don taga ta wulakantata.


Ku Biyo Mu A Shafukan Sada Zumunta🙏👏


www.instagram.com/idongari_tv


http://Www.twitter.com/idongari_tv


Www.youtube.com/idongaritv

Www.facebook.com/idongaritvADVERTISEMENT

Leave A Reply

Your email address will not be published.