Hadiza Gabon Ta Kusa Kashe Amina Amal Saboda Duka

2 360

ADVERTISEMENT

Tun bayan fadan jaruman masa’antar shirya fina- finai hausa ta kannywood Hadiza Aliyu Gabon da Jaruma Amina Muhammad Amal jama’a ke ta faman kace-nace.

Musamman bayan bayyanar wani faifen bidiyo ta na dukan Amal, hadi da yi mata tambayoyi, mutane da dama sunyi kira ga lauyoyin human right kan su shiga cikin wannan lamari.

Danna Alamar ja da Fari 👇 Don Kallon Cikakken Video, ko ku cigaba da karatun ka


Lauyoyin kare hakkin bil adaman sun nemi amal da ta yarda su kwato mata hakkinta kan wannan cin zarafi da hadiza gabon da kawayen ta sukayi mata. Inda har suka shigar da kara gabon kotu.

Takardan da lauyoyi sha biyu suka turawa ama kan in ta yarda su tsaya mata


A kwanakin baya, idongaritv ta yi rubutu akan, Amal ta kamu da rashin lafiya, sakamakon wannan duka da a ka yi ma ta, to amma bayanai sun nuna cewa, bangaren Gabon su na zargin cewa, karya ce kawai.

Bayan wata hira da jaridar LEADERSHIP tayi da daya daga cikin lauyoyin da suka tsaya wa amal, wato Barrister Nazir A. Uba, ya tabbatar da rashin lafiyar, inda yace har yanzu jarumar ta na fama da matsalar ji a kunnenta guda daya dalilin wannan duka da ta sha.

Ga Dai Yadda Tattaunawar Ta kasance:

Jaridar leadership: Za mu so mu ji dalilin da ya sa ku ka shigo cikin wannan batu na neman hakki.


Barrister Uba: kamar yadda na sha gaya wa mutane ’yan uwanku ’yan jaridu, Najeriya har yanzu ba ta yi lalacewar da mutum da zai yi laifi, kuma ya san laifi ne, ya dauka ya yi ‘posting’ ba. ko da laifin nan kasa ya shafa gabadaya ko kuma a’a jiha ya shafa ko karamar hukuma ko kuma hakki ne na wani.

To, saboda haka bayan mun ga an ci zarafin wannan yarinya, an dake ta, an zage ta, an yi ma ta kazafi a kan abinda ita, an ce ana zargin cewa ta yi, amma kuma ita ba ta yi ba, kuma duk duniya babu wani ‘post’ da ya fita ko na magana ko na wani abu. Mu dai ba mu gan shi ba, ba mu ji shi ba, wanda ya jawo a ka yi wannan cin zarafi da a ka yi ma ta.


To, wannan shi ne dalilin da ya sa bayan abubuwan sun fita, wata kungiya a can Amerika ta ga cewa ya kamata a zo a shigar wa yarinyar nan, saboda a na tunanin fada ne tsakanin mai karfi da maras karfi ko kuma mai kudi da talaka ko kuma sa ‘superstar’ da wacce ba ‘superstar’ ba misali.

Jaridar leadership: Wato ku na ganin akwai cin zali kenan?


Barrister Uba: Akwai cin zali cikakke a ciki. To, shi ne kungiyar ta neme mu kuma yanzu kofarmu a bude ta ke, saboda kullum sai na amsa waya akalla 15 zuwa 20 na lauyoyi daban-daban maza da mata da kungiyoyi da su ke son su shigo cikin wannan tafiya a yi da su, saboda su kansu ’yan wannan masana’anta ta Kannywood gata a ke yi mu su, idan a ka zo a ka nemi hakkinta. Idan kotu ta gamsu da abinda mu ke fada, ta ga ta cancanta, da a bi ma ta hakkinta, shikenan. Idan wannan kotu ta ce ba ta cancanta ba, to akwai kotuna a sama, za mu iya tafiya. Kuma wannan shi ne dalilin da ya sa muka shigo.


Jaridar Leadership: Kenan ka na so ka gaya wa duniya cewa, ba Amal ce ta nemi ku shigo ku nema ma ta hakkinta ba, a’a, ku a matsayinku na masu kare hakkin bil adama ne ku ka shigo?


Barrister Uba: Magana ta gaskiya kafin wannan shari’ar, Amal saidai na gan ta a allon talabijin ko kuma na ga labaranta a Youtube ko a fim din Hausa. Ban taba ganin ta a fili ba, ba ni da ‘contact’ dinta kuma ba ita ta neme mu ba.

Jaridar Leadership: To, amma mutane za su so su san wacce kungiya ce daga Amerika ta neme ku ta ke daukar nauyin shari’ar.

ADVERTISEMENT


Barrister Uba: To, wannan kungiyar sun bukaci mu boye sunansu, amma idan lokaci ya yi, wanda ya kamata a sani, za a sani, kuma mun yi mu su ‘undertaking’ cewa ba za mu bayyana su ba,
Saboda har yanzu a shari’ance dai bayan ‘issue’ na shari’a da a ka buga a jarida, ba a kai wa ita Gabon takardar kara ba, saboda a na cewa ba a yi ‘direction’ ba (wato tsayar da kotun da za ta yi shari’ar). Saboda haka abinda mu ka sani shi ne mun shigar da kara, mu na jiran a yi ‘direction’ ..mu ji wacce kotu ce za ta yi, mu je mu dauki rana mu sadar da ita Gabon da sammaci. Kuma abinda kotu ta yi, shikenan.

Jaridar leadership: bayan kun shigo cikin lamarin, shin kun nemi amincewar ita Amal din a kan za ku tsaya ma ta?

Barrister Uba: Eh, gaskiya mun yi wannan, kuma a rubuce ma ta yi, don kada a samu matsala ko tangarda ko kada wani ya zo ya zare ma ta idanu ko a nuna ma ta karfi ko wani abu ko wata yaudara, daga baya ta zo ta yi ‘disowning’ din mu, saboda an sha yin haka, shi ne mu ka sa ta rubuta takarda tun farko, wacce ita ce za ka ga ta na yawo, ta amince a lokaci lauyoyi 12 ne, ta amince a matsayin lauyoyinta.

Jaridar Leadership: Amma an ce a na kokarin a sulhunta maganar nan. Shin Gaskiya ne?

Barrister Uba: To, ka san har kullum shi sulhu alheri ne. Ko ba haka ba? Kuma kamar yadda na sha fada, a kowane mataki a shari’ance a na yin sulhu koda kuwa kotu ta yi hukunci za a iya zaunawa a yi sulhu tunda cikin yardar Allah a iya wannan mataki da a ke ciki na yanzu mun shigar da shari’ar neman hakki ne kawai kuma akwai yiwuwar za a sulhunta din, domin mun zauna ita uwar kungiyarsu (‘yan fim) ta MOPPAN mun fahimci juna. Mun yi magana da su cewa, za a zauna, idan sulhu ya yi, shikenan ba mu da damuwa.

Jaridar Leadership: To, ku na da wasu sharudda a wannan sulhu da za a yi?


Barrister Uba: Eh to, sharuddanmu ai su ne da ma abinda ya sa mu ka garzaya kotu, shi ne abinda a ka yiwa ita wannan yarinya da mu ka ga ba daidai ba ne, kuma mu ka roki kotu ta bi wa yarinyar nan hakkinta ta hanyar roko da mu ka yi a gaban kotu cewa ita Hadiza Gabon yakamata ta buga a manyan jaridu guda biyu wadanda a ke sayar da su a mataki a kasa cewa ta na neman afuwar Amal, sannan ta rubuta cewa da yawunta ita, ko ta sa wasu, ba za ta sake yi ba. Saboda ka san ba fa ita Hadiza Gabon kadai ce ta dake ta ba. Akwai sauran yaranta da direbobinta da duk wani wanda za ta iya ba wa umarni ya ji ko kuma ta hana shi ya hanu, ya taimaka wajen dukan wannan baiwar Allah.

Jaridar Leadership: To, amma a takardar da mu ka gani mun ga cewa ita Hadiza Gabon kadai ku ka kai kara, ba ku saka wadancan mutanen da ka ambata ba.


Barrister Uba: Wannan gaskiya ne, amma a shari’ance ba za ka kai mutumin da ba ka san shi ba kara. To, saboda haka idan mu ka sa sunan mutumin da ba mu sani ba, shari’ar tamu za ta iya samun tazgaro. Ita wannan (Hadiza) ita mu ka sani kuma duk abinda su ka yi da yawunta ne. To, saboda ha ka ita za mu iya sadarwa da sammaci kai-tsaye. Saboda haka wadancan mutane (a wajenmu) su na yi ne da yawunta.

Jaridar Leadership: To, ku kenan ku na nufin ko da a na cikin shari’ar ne idan ku ka gano akwai wane da wance a mutanen da a ka je da su a ka yi dukan, su ma za a shigar da su cikin shari’ar kenan?


Barrister Uba: Eh to, wannan kuma sai abinda hali ya kama… A shari’ance hakan zai iya yiwuwa. Akwai tunanin hakan.

Jaridar Leadership: To, yanzu kun kai ga mika wa rundunar ’yan sanda koken ta yi bincike kuma ta shigar da caji baya ga wannan shari’ar da neman diyya?

Barrister Uba: Eh, mu na shirin hakan sosai ma kuwa.

Jaridar Leadership: Ba ku kai ga mikawa ba?


Barrister Uba: Ba mu kai ga yin hakan ba, amma dai akwai hakan. Shirye-shirye sun yi nisa wajen yin hakan.

Jaridar Leadership: To, amma akwai batun shakkun cewa, bidiyon da a ka gani ba a ga fuskar ita Hadiza Gabon ba, sai muryarta, wanda hakan ke nuna cewa watakila ma ba ita ba ce.


Barrister Uba: Eh, akwai matakai sosai da sosai kuwa. Ka san sha’ani na bincike shi zai bayyana. Idan ita (Hadiza) ta musa, to mun tanadi hanyoyi wasu daban, mu na nan da hujjoji a tare, wadanda za su tabbatar da cewa ita din ce. Wannan su na nan a shirye mun shirya su kuma cikin yardar Allah za mu gabatar da su a wajen ’yan sanda ko a wajen hukumar kula da cin zarafin mata da kananan yara ta kasa ko kuma ma a wajen kowace hukuma ce mu ka kai, domin su tantance su gani. Idan su ka ce sun gamsu, sai su dauki matakin da su ka ga ya dace.

Duba Wannan: An gano Bayanan Sirri A Wayar Amina Amal, Tabbas Sharri Tayiwa Hadiza Gabon

Jaridar Leadership: A kwanakin baya an bayar da rahoton cewa, ita yarinyar nan Amal ta tsinci kanta a halin rashin lafiya. Shin meye gaskiyar wannan magana.


Barrister Uba: Wannan gaskiya ne, don lokacin da yarinyar nan ta zo Kano ma ta na cikin halin kaka-ni-ka-yi. Idan ta ci abinci, ta yi amai, a kara ma ta ruwa, a yi wane-a yi wane har ma mu ka fara tunanin ‘case’ din ma ba zai yiwu ba, saboda yanayin jikin. To, cikin yardar Allah dai jikin ya zo yau, gobe ya koma, amma dai alhamdulillahi yanzu babu matsala sosai, ta na iya yin magana, ta na iya cin abinci. Amma har yanzu ta na cewa, ba ta ji a kunnenta guda daya; ko na hagu ko na dama, inda a ka dake ta da takalmi da sanda da sauran abubuwa, wanda idan hali ya yi duk za mu gabatar a gaban kotu cikin yardar Allah.

Jaridar Leadership: Amma wasu su na son su san a wane asibiti a ka rike ta, saboda su na ganin kamar karya ne labarin da a ka buga na rashin lafiyar.

Barrister Uba: Wannan idan hali ya yi duk za mu sanar, amma abu ne na bincike; ba ma so mu bayar da satar amsa a kai. Ka san shi yaki dan zamba ne. To, ba zai yiwu gabadaya a ce duk shirye-shiryenmu ya zama mun yayatawa duniya ba. Amma idan hali ya yi za a san asibitin da su ka bincika su ka yi komai, domin akwai komai da komai an tanada, kuma cikin yardar za mu kawo gaban kotu.

DAGA IDONGARITV.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/idongaritv

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KaSCR0Vwn9HHJI2DSszGak

Instagram

Youtube

Twitter

ADVERTISEMENT

2 Comments
  1. Ahmad tashan mai alewa says

    To allah ya taimaki mai gaskiya

  2. Ahmad tashan mai alewa says

    Duk allah yataimaki mai gaskiya

Leave A Reply

Your email address will not be published.