Hadiza Gabon ta kara shiga matsala – kotu ta bada umarnin cafko ta kan kin amsa gayyatar kotu

0 72

ADVERTISEMENT

Ranar Alhamis 16 ga watan mayu, mai shari’a muntari dandago na kotun magistrate court 15 a kano ta bawa komishinan ‘yan sanda na jihar kano umarnin kamo fittaciyar jarumar wasan Hausa hadiza Gabon sabida taki amsa kiran kotun.

Mustapha naburaska shine ya shigar da karar jarumar kan zarginta da cewa tanayi masa barazana da rayuwa ya yanke shawarar maka ta kai tsaye zuwa kotu saboda saboda yana tsoron idan ya kaiwa hukumar ‘yan sanda baza ta dauki mataki akanta ba.

“kasancewar jarumar tayi suna kuma tana da abokai daga cikin jami’an ‘yan sanda da kuma manyan ‘yan siyasa da masu kudi a fadin kasar nan.”

Alkalin kotun Majistare da ke Muntari Dandago ya umurci kwamishinan ‘yan sanda na Kano, Muhammad Wakili wanda akafi sani da Singham ya kamo jarumar tunda ya ki amsa gayyatar kotu.

DUBA WANNAN 👇

“Tunda wacce aka yi kara ba ta da shirin amsa gayyatar kotu, Ina umurtar kwamishinan ‘yan sanda ya sanya a kamo wacce aka gayyata kotun.

“Ina kuma umurtan kwamishinan ‘yan sandan ya gudanar da bincike kan zargin da mai shigar da kara ya yi idan an samu gaskiya ciki sai a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kuliya domin ta fuskanci shari’a.”

ADVERTISEMENT

Kalli Video👇

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>>
https://chat.whatsapp.com/KaSCR0Vwn9HHJI2DSszGak

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/idongari_tv

Instagram: https://instagram.com/idongari_tv

Twitter: https://twitter.com/idon_garitv

Youtube: https://www.youtube.com/idongaritv

ADVERTISEMENT

Leave A Reply

Your email address will not be published.