Ganduje Bala’i Ne Da Allah Ya Turowa Mutanen Kano – Diyar Sarkin Kano

1 37

ADVERTISEMENT

Yar gidan Sarkin Kano ta mayarwa da Ganduje raddi inda ta bayyana gwamnan Kano Ganduje a matsayin “Bala’i da Allah ya kawowa mutanen Kano”.

Yayin da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kammala kacaccala jihar kano zuwa masarautu biyar, diyar Sarkin Kano, shahida ta yiwa gwamnan raddi akan abinda ya yiwa mahaifinta.

A jiya 11 ga watan afrilun 2019, diyar sarkin kano ta wallafa hoton gwamnan kano, Abdullahi umar ganduje a shafin ta na instagram kana tayi rubutu akasan wannan hoton inda tace “Idan kuna so ku ga me rashin asali ke jawowa ku duba ku ga abinda Ganduje yake yi a Kano.

” Mutumin da bashi da wata daraja, amma yana kokarin ya ja da mutanen da suke da daraja. Ina addu’ar Allah yasa kada mahaifiyata ta ce na goge wannan bayanin a shafina.

“Ganduje shi ne bala’in da yafi komai a jihar Kano. Abinda yake yi a gwamnatinsa, son rai ne kawai a ciki. Bamu kamaci gwamnati irin wannan ba. Allah ya raba mu da masifar Ganduje dan kuwa mutanen da basu da asali sune suke bata masu asali.”

KU DUBA WANNAN: Naziru sarkin waka yayi martani mai zafi ga ganduje kan raba masarautar kano

Bugu da kari, Shahida ta kara rubuta cewa, “Da zarar Sarki ya tsorata da rasa kujerar sa, abinda yake yi shine ya sauke kansa,”

Wannan bayani da shaheeda tayi, tabbas ya jawo cece kuce da maganganu maras dadin ji. Sai kuma, daga baya ta goge.

Amma ‘yar uwarta Fulani Siddika, ta sake sanyawa a shafinta. Bayan ta daura ne, tayi rubutu akasa inda tace “Ba ni da wani abu da zan ce gaskiya!” ‘Yar’uwata ta riga ta fada duka.”

ADVERTISEMENTDaga IDONGARITV

Ku biyo mu a Facebook: facebook.com/idongaritv

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>>

https://chat.whatsapp.com/KaSCR0Vwn9HHJI2DSszGaI

Youtube.com/idongaritv

Instagram.com/idongari_tv

Twitter.com/idongari_tv

ADVERTISEMENT

1 Comment
  1. Jamilu Isah says

    Allah ya kiyaye

Leave A Reply

Your email address will not be published.