An Baiwa Aminu Ado Bayero Sarautar Bichi Bayan An Raba Masarautar Kano

0 24

ADVERTISEMENT

Wasu majiyoyi masu karfi daga gidan sarautar Kano da kuma gwamnatin jihar, sun tabbatar wa BBC cewa, Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bai wa Aminu Ado Bayero sarautar daya daga cikin sababbin masarautun da aka kirkiro a Kano.

An bai wa Aminu Ado Bayero, dan marigayi Sarki Ado Beyeron sarautar Bichi ne a yau juma’a, 10 ga watan mayu.

Wani na kusa da sabon sarkin Bichin da ya bukaci a boye sunansa ya tabbatar wa BBC lamarin ya kuma ce tuni Aminu Bayeron ya karbi sarautar.

Mai martaba sabon sarkin Bichin shi ne Wamban Kano a yanzu, kuma yana daya daga cikin manyan ‘ya’yan marigayi Ado Bayero. Nan gaba ne dai ake sa ran za’a sanar da nadin nasa.

Wasu bayanai dai sun nuna cewa tuni ‘yan gidan sarautar Kano suka yi ta kamun kafa a wajen gwamna don ganin an nada su sarautar.

A ranar Laraba ne Gwamna Ganduje ya sanya hannu kan dokar da majalisar dokokin jihar ta gabatar a ranar Litinin, ta neman kara yawan masarautun jihar.

Lamarin dai ya janyo ce-ce ku-ce a tsakanin al’ummar kasar baki daya ba ma na Kano ba kawai.

Source: bbchausa.com

Daga IDONGARITV.COM

Ku biyo mu a Facebook: facebook.com/idongaritv

ADVERTISEMENT

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>>

https://chat.whatsapp.com/KaSCR0Vwn9HHJI2DSszGaI

Youtube.com/idongaritv

Instagram.com/idongari_tv

Twitter.com/idongari_tv

ADVERTISEMENT

Leave A Reply

Your email address will not be published.