Abinda Ake Gudu Ya Afku: Dogaran Sarkin Kano Sun Fara Guduwa Suna Komawa Masarautar Bichi

0 45

ADVERTISEMENT

Zirga-zirga ta ragu sosai a fadar Sarkin Kano, Muhammad Sanusi na II, tun bayan da aka kammala kaddamar da sababbin masarautun guda hudu da gwamna Ganduje ya yi wanda suka hada da Bichi, Rano, Karaye da kuma Gaya.

Jaridar legit.ng ta rawaito cewa “sun samu rahoton cewa tun bayan dawowar sarkin daga kasa mai tsarki ya kadaice kanshi a daki baya magana da kowa”

Fadar a cike take da jama’a ranar Lahadin da ta gabata a lokacin da sarkin ya dawo daga aikin Umrah, inda mutane da dama sukaje har filin tashi da saukar jirage na Mallam Aminu Kano suna yi mishi barka da
Zuwa.

Mutanen sun biyo shi har zuwa fad daga filin jirgin, inda suke ta yi mishi kirarin “Sarki Mai Martaba.”

Rahotanni sun tabbatar da cewa a yau Talata zirga-zirga ta ragu sosai a fadar, duk yawan zirga-zirgar da aka saba gani a fadar ta mutane da ababen hawa komai ya ragu. Mutane kalilan ne suka rage a fadar sai ma’aikatan fadar.

Wani ma’aikaci a gidan sarkin wanda ya yi magana da manema labarai kuma ya bukaci a boye sunansa, ya tabbatar da cewar sarkin ya zabi ya kadaice kanshi tun dawowar shi daga kasa mai tsarki.

Ya ce: “Tun dawowar Mai Martaba, bai sake magana ba. Ya samu ganin baki kalilan ne da suke zuwa ziyartar shi. Manema labarai da yawa sun zo domin yin hira da shi amma ya hana kowa ganinshi.

“Wannan kirkiro sabbin masarautu ya shafi yawaitar zirga-zirga a fadar nan, kuma ina mai tabbatar muku cewa Mai Martaba bai ji dadin abinda ya faru ba.”

A cewar shi, Dogarai da yawa da suke fadar Sarkin Kanon sun bar fadar zuwa sauran masarautun da aka kirkira, musamman ma masarautar Bichi inda dan gidan Marigayi Ado Bayero ke Mulka.

Shin me zaku ce? Menene ra’ayinku?

ADVERTISEMENT

Ku biyo mu a Facebook: facebook.com/idongaritv

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu da duminsu whatsapp>>>>>>>>>https://chat.whatsapp.com/KaSCR0Vwn9HHJI2DSszGaI

Youtube: Youtube.com/idongaritv

Instagram: Instagram.com/idongari_tv

Twitter: Twitter.com/idongari_tv

Zaku iya tuntubarmu ta email [email protected]

Source: legit.ng

ADVERTISEMENT

Leave A Reply

Your email address will not be published.