Jaruma tayiwa dan takarar gwamnan Gombe Yusuf Chikaire fata – fata kan bashin da take binsa har naira miliyan 13,000,000

0

Shahararriyar mai saida kayan mata, jaruma tayiwa dan takarar gwamnan Gombe Yusuf Chikaire fata – fata kan bashin da take binsa na mukudan kudi naira na gugan naira har miliyan goma sha uku (N13,000000)

Jaruma ta bayyana hakan ne a shafinta na Instagram inda ta kira Yusuf Chikaire,  ta bayyana cewa tana binsa makudan kudade har naira miliyan 13 ya biya ta hakkinta in har yana son zaman lafiya.

Jaruma da take bada labarin haduwarta dashi, ta bayyana cewa, Yusuf Chikaire ya samu kyautar gida a shekarar 2010, kuma bisa yarjejeniya ta kawo masa wasu hamshakan attajirai guda uku domin su sayi gidan, ta ce sun amince akan bata kaso 5% na kudin da aka sayar da gidan shine miliyan 13 kuma yau kusan wata 11 kenan amma shiru.

Jaruma a karshe ta fallasa cewa ” bashi ce tasaka shi ya gudu ya bar PDP ya koma APC har yana takarar neman gwamna a garin gombe, to ita ta ci alwashi sai ta karya masa kudirinsa na zama gwamna.”

 

Jaruma mai kayan mata tayiwa dan takarar gwamnan Gombe Yusuf Chikaire fata - fata kan bashin da take binsa har naira miliyan 13,000,000

"Jaruma" "yusuf chikaire"

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here